Friday

Home › › Shugaba Buhari zai dawo Yau Juma’a – Femi Adesina









Shugaban Muhammadu Buhari zai dawo Yau, Juma’a. Wannan ya bayyana ne ta shafin sada zumunta da ra’ayin mai Magana da yawun shugaba kasa, Mr. Femi Adesina.

Karanta jawabin:

Ana sa ran dawowar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, A Yau Juma’a, 10 ga watan Maris 2017.

Shugaban kasan ya bar kasan ne ranan 19 ga watan Junairu, 2017 domin hutu sannan ya ga likita. An jinkirta ranan dawowarsa ne bisa ga shawaran likitoci na cewa ya sake hutawa.

  • KARANTA WANNAN: Uwar Gidan Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Shugaba Muhd Buhari.


  • Shugaba Buhari yana mika godiyarsa ga "yan Najeriya da kewaye wadanda suka yi masa addu’a da kuma mika gaisuwarsu.”

    SANARWA DAGA FEMI ADESINA

    Mai Magana da yawun shugaban kasa.
    March 9, 2017.






  • No comments:
    Write Comments