Monday

Home › › Jerin shugabannin Arewa wadanda aka zarga da neman kujerar mataimakin shugaban kasa yayin da ake duba lafiyar Buhari a london.

Yayinda aka daga hutun ganin likita na shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kwanaki 51, sannan kuma jita-jita ya ci gaba da yaduwa, ana ta tsoro kan cewa babu mamaki ba zai dawo ba.
Ana ta rade-radin cewa idan bai dawo ba, dole wani ya zamo mataimakin shugaban kasa ga Yemi Osinbajo.

Babu shakka dawowar shugaban kasa Buhari ya dakatar da dukkan abubuwan, amma dai ya zo cewa masu ruguza karfin siyasa a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun riga sun fara tattara jerin mutanen da zasu maye gurbin babban matsayi na biyu a kasar.



Ga wasu daga cikin sunayen a kasa:


KARANTA WANNAN :- Sabuwar Wakar Baba Buhari: Baban chinedu


  • 1. Muhammadu Sanusi II, sarkin Kano


  • Muhammadu Sanusi II

    An haifi Sarki Muhammadu Sanusi II wanda aka fi sani da Sanusi Lamido Sanusi a ranar 3i ga watan Yuli, 1961 sannan kuma a yanzu shine sarkin masarautar Kano, inda ya dare kujerar sarautar a ranar 8 ga watan Yuni, 2014.
    An nada masa sarautar Kano ne bayan rasuwan kanin kakansa Ado Bayero, wanda ya rasu a ranar 6 ga watan Yuni, 2014. Ya kuma kasance tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya.




  • 2. Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan jihar Sakkwato



  • Aminu Waziri Tambuwal

    An haifi Aminu Waziri Tambuwal a ranar 10 ga watan Junairu, 1966 sannan kuma shine Gwamnan jihar Sakkwato. Ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai na Najeriya.

    Dan jam’iyyar APC, kuma wakilin mazabar Tambuwal/Kebbe na jihar Sakkwato, a lokacin da yake majalisar wakilai.





  • 3. Nasir El-Rufai, Gwamnan jihar Kaduna


  • Nasir El-Rufai


    An haifi Mallam Nasir Ahmad El-Rufai a ranar 16 ga watan Fabrairu, 1960 sannan kuma ya kasance Gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban wata hukuma mai zaman kanta a Najeriya.
    Mutane da dama sun yarda da cewa shine na hannun daman shugaban kasa Buhari sannan ya kuma kasance tsohon ministan babban birnin tarayya, Abuja daga 2003 zuwa 2007.




  • 4. Bukola Saraki, Shugaban majalisar dattawa


  • Bukola Saraki

    Bukola Saraki ya kasance dan siyasar Najeriya wadda ke shugabantar majalisar dattawan Najeriya tun 2015. A baya ya kasance Gwamnan jihar Kwara daga 2003 zuwa 2011.




  • 5. Mallam Nuhu Ribadu, Tsohon shugaban hukumar EFCC

  • Mallam Nuhu Ribadu.

    An haifi mallam Nuhu Ribadu a ranar 21 ga watan Nuwamba, 1960. Ya kasance shugaban kungiyar kula da kudin shiga na man fetur kuma tsohon jami’in gwamnatin Najeriya mai yaki da cin hanci da rashawa, ya kuma kasance tsohon shugaban hukumar EFCC.







    No comments:
    Write Comments