Friday

Home "Dolene Fa Buhari Ya Mike Tsaye" : inji el-rufa'i
Abubuwa na neman ya kwace ma Buhari, dole ya mike tsaye – Inji Gwamnan kaduna El-Rufai



Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari wadansu daga cikin na kusa dashi kamar sakataren gwamnatin tarayya, David Babachir da Abba Kyari suna yin yadda suka da ma a gwamnatin.

El-Rufai ya fadi hakanne a wata takarda da ya rubuta wa shugaban kasa domin gaya masa yadda ya kamata ya mulki kasa Najeriya sannan kuma da sanar da shi yadda ya bari abubuwa ke ta tabarbarewa a kasa Najeriya.

Yace Buhari ya yi watsi da irin manufofin da suka yarda akai a lokacin da aka kafa jam’iyyar sannan kuma nuna da rashin ko in kula da neman shawara daga gwamnonin jam’iyyar masu ci da wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a wancan lokacin.

KARANTA WANNAN:- PDP Ta Yi 'Karar Wani Sanata Salamakon Canza Sheka da yayi

El-Rufai yace ita kanta jam’iyyar APC din a watse take saboda Buhari ya kasa rike ta a matsayinsa na shugaban kasa.

Yace a gaskiya jam’iyyar su ta APC ta kasa cika alkuwarran da ta dauka wa mutane. “Bayan nasarorin da akasamu a yaki da Boko Haram da yaki da cin han ci da rashawa babu wani abu da akayi domin talakawa a kasa Najeriya.”

“ Hakan zai iya zama ba shirin ka bane amma mutane daga nesa haka suke gani”

“ Wadannan ‘yan siyasar kansu kawai suka sani amma bawai jam’iyyar ko kuma ‘ya’yan jam’iyyar ba”

“ Sakataren gwamnatin tarayya bai san komai ba akan siyasa sannan kuma baya ganin kowa da gashi. Yana taka duk wanda yaso a jam’iyyar, gwamnane kai ko jigo a jam’iyyar APC din.

“ Ana ta yada zantuttuka a jaridu cewa wai ba ka da iko a gwamnatinka sannan sai yadda wasu suka yi da kai a gwamnati.”


El-Rufai yaba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari akan yadda zai gyara kasa Najeriya musamman fannin Ilimi, sufuri da kiwon lafiya.

El-Rufai yace dole ne Buhari ya sanarwa ‘yan Najeriya abubuwan da ya shirya domin samun nasara a mulkinsa.

Ya yi kira ga shugaban kasa da ya sake fitowa takara a 2019.

Ya kara da cewa dole ne fa gwamnatin nan ta yi nasara “ko domin mu da muka amfana da farinjinin Buhari.”











No comments:
Write Comments